Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane 21 a Zamfara

'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a Zamfara
'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a Zamfara Jakarta Globe

‘Yan bindiga sun kashe mutane 21 tare da raunata 12 a wani farmaki da suka kaddamar kan kauyukan kananan hukumomin Maru da Talata Mafara a jihar Zamfara.

Talla

Mai Magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, Mohammed Shehu ya ce, maharan sun far wa Tungar Malan da Manyan Karaje da Tungar Arne da Dangodon Maiyakane da Dangodon Mai Masallaci da kuma Boleke a Karamar Hukumar Maru da zummar satar shanu.

Sai dai bata-garin sun fara harbi kan mai uwa da wabi bayan mayakan sa-kai sun tunkare su, lamarin da ya yi sanadin ajalin mutane 15 nan take.

A bangare guda, ‘yan bindigar sun sake kashe mutane shida a kauyukan Gidan Dan Kani da Tungar Lauti da Inwala da Dangodo a Karamar Hukumar Talata Mafara.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce, an kashe mutanen shida ne a kan hanyarsu ta dawowa daga wata jana’iza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.