'Yan fashi sun kashe 'yan sanda 8 a Najeriya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Bayanai daga Najeriya na cewa, wasu gaggan 'yan fashi dauke da muggan makamai sun kashe jami'an 'yan sanda 8 cikinsu har da mai mukamin DPO bayan sun afka wa bankin First Bank da ke garin Isanlu a jihar Kogi.
Har ila yau, wata mata ta rasa ranta sakamakon harsashin bindiga da ya same ta a yayin musayar wuta tsakanin 'yan fashin da jami'an 'yan sandan a cewar rahotanni.
Kawo yanzu babu cikakken bayani game da lamarin da kuma adadin rayukan da suka salwanta, amma an ce, barayin sun kashe hatta wasu daga cikin ma'aikatan bankin da kwastamominsu.
Yanzu haka rundunar 'yan sanda ta dukufa wajen gudanar da cikakken bincike kafin ta yi karin bayani game da lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu