Najeriya

Cibiyoyin killace masu coronavirus sun cika makil

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, tare da mataimakinsa Obafemi Hamzat daga hadu, sai kuma kwamishinansa na lafiya Farfesa Akin Abayomi.
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, tare da mataimakinsa Obafemi Hamzat daga hadu, sai kuma kwamishinansa na lafiya Farfesa Akin Abayomi. LASG

Gwamnatin Jihar Lagos da ke Najeriya ta garagadi cewa, muddin jihar ta ci gaba da samun alkalumann mutane 200 zuwa 300 da ke kamuwa da cutar coronavirus, to babu shakka za ta rasa wuraren killace masu dauke da cutar na kusa.

Talla

Gwamnatin ta bayyana cewa, wadanda cutarsu ta tsananta za ta ci gaba da kula da su a cibiyoyin da take da su, inda kuma masu dan dama-dama za a koma da su gidajensu don ci gaba da samun kulawa a can.

Jihar Lagos ce ke kan gaba wajen fama da ibtila’in coronavirus a Najeriya, inda take da jumullar mutane dubu 5 da 663 da suka harbu da kwayar cutar.

A jumulce, mutane dubu 11 da 844 suka da kwayar cutar coronavirus a Najeriya baki daya kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Yaduwar Cutuka ta kasar suka nuna yazuwa daren jiya Juma'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI