Najeriya

Mun kashe barayin shanu 70-Sojin Najeriya

Dakarun sojin Najeriya
Dakarun sojin Najeriya REUTERS/Warren Strobel

Rundunar Sojin Najeriya ta ce, ta kashe a kalla barayin shanu 70 a dajin Kachia da ke jihar Kaduna bayan wani aiki da ta kaddamar a jiya Juma’a a yankin.

Talla

Mai magana da yawun sojin kasar, Manjo Janar John Eneche, ya ce, rundunar Operation Thunderstrike ne ta kaddamar da aikin tare da hadin guiwar mayakan sa-kai.

Yanzu haka sojojin na ci gaba da laluben sauran barayin shanun da suka buya a dajin na Kachia a cewar Manjo Janar Eneche.

Jihar Kaduna da wasu sassan arewacin Najeriya na fama da hare-haren ‘yan bindiga masu satar shanu tare da yi wa jama'a kisan gilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.