Najeriya

Kwanaki 100 da fara bullar coronavirus a Najeriya

A ranar 27 ga watan Fabairu cutar coronavirus ta fara bayyana a Najeriya
A ranar 27 ga watan Fabairu cutar coronavirus ta fara bayyana a Najeriya 237online

A yayin da aka cika kwanaki 100 da fara bullar Covid-19 a Najeriya, a kalla mutane dubu 12 da 233 suka kamu da kwayar cutar a kasar.

Talla

A ranar 27 ga watan Fabairun da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta tabbatar da mutun na farko dauke da cutar.

Alkaluman Hukumar Yaki da Yaduwar Cutuka ta kasar sun nuna cewa, ko a jiya kadai, an samu mutane 389 da suka harbu da cutar a jihohi 23, sannan mutane tara sun sake rasa rayukansu a jiyan.

Mutane dubu 3 da 826 ne dai suka yi katarin warkewa daga wannan annoba a Najeriya, yayin da a halin yanzu, mutane dubu 8 da 65 ke ci gaba da samun kulawa, sai kuma 342 da suka mutu sakamakon cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI