Bankin Afrika ya baiwa Najeriya rancen dala miliyan 288
Bankin raya kasashen Afrika na AFDB ya ce ya baiwa Najeriyar rancen dala miliyan 288 a ‘yan tsakanin nan don taimakawa kasar farfadowa daga illar da annobar COVID-19 ta yiwa tattalin arzikinta.
Wallafawa ranar:
Gabanin ikirarin bankin na AFDB ko a watan jiya ministar tattalin arzikin Najeriyar ta bayyana yiwuwar tattalin arzikin kasar ya fuskanci koma baya da kashi 9 sanadiyyar annobar ta COVID-19 da ta tilasta kulle muhimman sassan kasuwanci da tattalin arziki baya ga farashin danyen man fetur da ya fadi a kasuwar duniya.
Ko cikin watan Afrilu Najeriyar mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afrika sai da ta karbi makamancin lamunin farfado da tattalin arzikin daga asusun bada lamuni na duniya IMF da yawansa ya kai dala biliyan 3 miliyan dari 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu