Kashi 42 na ma'aikata sun rasa aiki a Najeriya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta ce, a kalla mutane 42 cikin 10 da ke kasar sun rasa gurabun ayyukansu a watan Afrilu sakamakon annobar coronavirus wadda ta addabi duniya.
Hukumar ta ce, wannan ya nuna cewar, kashi 42 na al’ummar kasar da ke aiki kafin watan Afrilun suka rasa ayyukansu kamar yadda binciken da ta gudanar ya nuna.
Rahotan hukumar ya ce, daga cikin mutane 10 da aka yi wa tambayoyi, 8 sun shaida mata cewar, kudaden da suke samu sun ragu daga tsakiyar Maris zuwa watan Afrilu, yayin da wasu suka gaza sayen kayan abincin da suka saba saye.
Annobar coronavirus ta yi sanadiyar rasa ayyukan miliyoyin mutane a fadin duniya, inda a kasar Amurka kawai mutane sama da miliyan 40 suka rasa aikinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu