Najeriya

'Yan Biafra na bata mana suna a duniya- Najeriya

Wasu 'yan kungiyar IPOB masu ra'ayin kafa kasar Biafra
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu ra'ayin kafa kasar Biafra http://naijagists.com

Gwamnatin Najeriya ta yi zargin cewa, kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biafra na kashe Fam dubu 85 a kowanne wata domin bata sunan Najeriya a kasashen duniya musamman a Amurka da Turai.

Talla

Sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar mai dauke da sanya hannun Garba Shehu ta ce, haramtacciyar kungiyar da ke alakanta kanta da addinin Yahudanci yanzu haka, na shela a kasashen duniya cewa, gwamnatin Najeriya na cin zarafin mabiya addinin Kirista a sassan kasar.

Sanarwar ta ce, tuni wasu daga cikin kasashen duniya suka fara yarda da farfagandar kungiyar wadda ke neman ganin kasar Amurka ta nada jakada na musamman domin gudanar da bincike kan lamarin.

Gwamnatin Najeriya ta ce, binciken da wata hukumarta ta gudanar tare da abokan huldarta na kasashen duniya, ya nuna cewar kungiyar na kashe Fam dubu 85 a kowanne wata wajen yada wannan farfagandar da ke bata wa Najeriya suna tun daga watan Oktoban shekarar 2019.

Shehu ya ce, fadar shugaban kasa na janyo hankalin 'yan Najeriya da kasashen duniya kan wannan farfagandar da ke neman raba kan jama’ar Najeriya da kungiyar ta IPOB ke yi kan zargin karya mara tushe.

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar ta IPOB wadda ta bayyana a matsayin kungiyar 'yan ta’adda, yayin da shugabanta Nnamdi Kanu ya tsere daga kasar bayan an bada belinsa a kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.