'Yan Boko Haram sun halaka sojojin Najeriya
Wallafawa ranar:
Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 6 a wani hari da suka kai kan sansaninsu da ke garin Auno a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.
Wata majiyar soji ta tabbatar wa manema labarai cewa, da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Asabar, ‘yan ta’addar suka kai farmakin tare da kashe sojojin, inda aka shafe tsawon sa’o’i biyu ana dauki-ba-dadi tsakanin bangarorin biyu.
Majiyar ta ce, mayakan sun ci galabar sojojin a wannan gumurzun, abin da ya sa sojojin na Najeriya suka warwatse.
‘Yan ta’addar sun kuma kwashe makamai tare da kona gidaje kafin daga bisani sojin sama na Najeriya su kawo dauki, inda suka fatattaki mayakan.
Yanzu haka, ana ci gaba da neman sojoji 45 da ba a gan su ba, amma ana kyautata zaton sun tsere ne domin buya a cewar majiyar tsaron.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu