Tattaunawa da ra'ayoyin masu sauraro kan matakin Buhari na janye batun sakin mara ga majalisun jihohi

Sauti 14:59
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase

Shirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan rana tare da Zainab Ibrahim, ya tattauna ne dangane da matakin shugaban Najeriya Mohammadu Buhari kan janye shirin sakarwa majalisun jihohi da bangaren shari'a mara, mako guda bayan sanya hannu akan dokar da zata tabbatar da hakan, bayan ganawa da shugaban ya yi da tawagar Gwamnonin kasar wadanda ke adawa da shirin, duk kuwa da farin cikin da ‘yan Najeriya suka bayyana a kan matakin.