Najeriya-Coronavirus

Coronavirus ta kashe mutane 17 cikin sa'o'i 24 a Najeriya

Jami'an kula da annobar korona a Najeriya
Jami'an kula da annobar korona a Najeriya Kola Sulaimon / AFP

Hukumar Yaki da cututtuka a Najeriya tace mutane 17 suka mutu jiya, yayin da 409 suka kamu da cutar coronavirus a fadin kasar.

Talla

Hukumar tace daga cikin sabbin mutanen 201 sun fito ne daga lagos, 85 daga Abuja, 22 daga Delta, 16 a Edo, jihohin Nasarawa da Borno da Kaduna, kuwannensu nada 14-14, Bauchi na da 10, Kano nada 5,  sai Kebbi da Plateau da 2 - 2.

A ranar 27 ga watan Fabairun da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta tabbatar da mutun na farko da ke dauke da cutar a kasar, inda ya zuwa yanzu Najeriya ta samu mutane 13,873 da suka kamu da cutar, 382 sun mutu, yayin da 4,351 sun warke.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI