Trump zai sanyawa jami'an ICC takunkumi kan tuhumar Sojin Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umurnin sanya takunkumi kan jami’an kotun hukunta manyan laifuffuka ta ICC da ke binciken zargin cin zarafin bil adama da ake yiwa sojojin kasar a Afghansitan wadanda ke da nasaba da laifuffukan yaki.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun fadar shugaban Amurka Kayleigh McEnany ya ce Rasha ce ke ingiza hukumar mara kima wajen gudanar da binciken da zummar batawa kasar da sojinta suna.
Trump ya kuma baiwa Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo umurnin hana jami’an kotun duniyar izinin shiga Amurka.
Shugaba Trump ya dade yana sukar kotun wadda ke shari’ar cin zarafin da kasashe suka kau da kai.
Kasar Afghanistan na daga cikin kasashen da suka amince da halarci kotun, yayin da gwamnatin Amurka take sahun gaba wajen kin amincewa da ita amma kuma tana tasa keyar yan wasu kasashe domin yi musu shari’a a cikin ta.
Babbar Mai Gabatar da kara a Kotun Fatou Bensouda ta ce ta na da hurumin gudanar da bincike kan zargin laifin da sojojin Amurka suka aikata a Afghanistan tsakanin shekarar 2003 zuwa 2014, cikin su harda kisan fararen hular da mayakan Taliban suka yi da kuma azabtar da firsinoni da sojin Afghanistan suka yi tare da taimakon sojin Amurka da jami’an hukumar CIA.
Amurka ta yi zargin cewar cin hanci da rashawa ya dabaibaye jami’an kotun wadanda ke bukatar gudanar da binciken.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu