Mun samu nasarori da dama - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin jawabi ga 'yan kasa kan ranar Dimokradiya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin jawabi ga 'yan kasa kan ranar Dimokradiya © Nigeria Presidency

Yau 12 ga watan Yuni take ranar Dimokradiya a Najeriya, ranar da dama ke da tarihi ga ‘yan kasar da ake kira June 12 a Turance, saboda a ranar ce gwamanin mulkin sojin Najariya ta gudanar da zaben na1993, ko da dai ba’a sanar da wanda ya lashe zaben ba, sakamakon soke zaben da shugaban mulkin sojan Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi.

Talla

To sai dai anyi yakinin cewa dan takarar jam'iyyar SDP, wato Moshood Olawale Abiola, ne ya lashe zaben da gagarumin rinjaye bayan dike abokin karawarsa na jam'iyyar NRC wato Bashir Othman Tofa.

Soke zaben dai ya haifar da gagarumanin bore masamman daga 'yan gwagwarmayar rajin kafa gwamnatin farar hula a wancan lokaci, lamarin da ya kai ga tsare mutane da dama ciki harda MKO Abiola.

Duk da cewa ana bukin wannan rana ta 12 ga watan Yuni a Najeriya ko wace shekara tun bayan kafuwar gwmnatin Dimokrdaiya a shekarar 1999, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara mata karfi wajen maida ita ranar Dimokaradiya a shekarar 2018, mai makon 29 ga watan Mayu da aka saba a kasar, sauyin ranar da ya tada hankalin wasu ‘yan Najeriya.

Duk da cewa gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ga Najeriyar kamar yadda aka saba, a wannan karon dai bukin na zuwa ne adai-dai lokacin da ake fama da annobar korona, da zai rage armashin sa.

A jawabin sa ga ‘yan kasar Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, bayan jinjina ga ‘yan mazan jiya da sukayi gwagwarmayar ‘yan Najeriya da wandanda suka tabbatar da Dimokradiya ciki harda ‘yan jaridu, shugaban yayi waiwaye kan rasarori da gwamnatinsa ta samu a shekarun da ya kwashe da kuma kalubale da ake fuskanta.

Cikin jawabin nasa shugaban Buhari ya bayyana samun nasarori kan muhimman manufofin da gwamnatinsa ta fi baiwa fifiko guda 9, ciki harda harkokin tsaro da yaki da cin hanci da rahawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI