Najeriya

Rashin shaidar kammala karatu ne suka sanya dakatar da Obaseki- APC

Shugaban Jam'iyyar APC na kasa Adams Oshoimhole.
Shugaban Jam'iyyar APC na kasa Adams Oshoimhole. Daily Post Nigeria

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da dalilan da ya sa ta haramtawa Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki sake takarar zaben gwamnan da za’ayi a watan Satumba mai zuwa.

Talla

Shugaban kwamitin tantance 'yan takarar Farfesa Jonathan Ayuba ya ce sun dauki matakin ne sakamakon matsalar da suka gano a takardun shaidar kammala karatun Gwamnan da ya gabatar musu.

Shugaban kwamitin ya ce gwamnan ya kasa gabatar da takardar shaidar kamala karatun da yayi a Cibiyar ilimi ta Benin sai dai wata wasika kawai ya gabatar wadda ke bayyana cewar ya je makarantar.

Farfesa Ayuba ya kuma ce kwamitin ya nuna shakku kan sahihancin takardar kamala bautar kasa da kuma karar da Gwamnan ya kai shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomhole a gaban kotu.

Kwamitin yace Obaseki tare da sauran yan takarar biyu da aka haramtawa tsayawa zaben fidda gwanin na iya daukaka kara.

Sai dai Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki yace ba zai daukaka kara ba, duk da yake bai bayyana matakan da yake shirin dauka ba.

Rahotanni sun ce Gwamnan na nazarin sauya sheka duk da goyan bayan da sauran Gwamnonin Jam’iyyar APC ke bashi na ganin ya zarce a zabe mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI