Gara da APC ta hana Obaseki takara - Ganduje
Wallafawa ranar:
Gwamnan Jihar Kano dake Najeriya Abdullahi Umar Ganduje yace jam’iyyar APC ta yi daidai wajen hana takwaran sa na Jihar Edo, Godwin Obaseki izinin sake takara a zabe mai zuwa.
Ganduje yace Jam’iyyar tabi matakan da suka dace wajen daukar matakkin kuma su yanzu abinda ke gaban su shine samun nasarar zaben da sabon dan takarar da Jam’iyyar zata tsayar.
Gwamnan yace Jihar Kano za tayi iya bakin kokarin ta wajen ganin Jam’iyyar APC ta lashe kujerar gwamnan jihar Edo saboda yadda aka bi matakan da suka dace daki daki.
A nashin bangaren, Gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike ya cacaki shugabannin Jam’iyyar APC kan matakin da suka dauka na haramtawa Godwin Obaseki takara, inda yace zai yi iya bakin kokarin sa wajen ganin Gwamnan ya lashe zabe mai zuwa.
Rahotanni sun ce Jam’iyyar PDP na zawarcin Obaseki amma Gwamnan yace ba zai yanke hukunci kan makoma sa ba har sai ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari nan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu