Likitoci a Najeriya sun tsunduma yajin aiki yayinda korona ke karuwa

Ma'aikatar lafiya da ke kula da masu cutar coronavirus a Maiduguri na Jahar Borno a Najeriya
Ma'aikatar lafiya da ke kula da masu cutar coronavirus a Maiduguri na Jahar Borno a Najeriya AFP

Likitoci a Najeriya yau sun tsunduma cikin yakin aiki saboda abinda suka kira kin gwamnati na biyan su hakkokin su da kuam samar musu da kayan aiki, a daidai lokacin da annobar coronavirus ke cigaba da yaduwa a kasar.

Talla

Kungiyar likitocin tace yayan ta dake aiki da gwamnatin Najeriya sun yanke hukuncin fara yajin aikin domin nuna rashin amincewar su da matakin na gwamnati, sai dai sun ce yajin bai shafi takwarorin su dake aiki a cibiyar yaki da masu fama da cutar coronavirus ba.

Akalla ma’aikatan lafiya 800 suka kamu da cutar coronavirus a kokarin da suke na yaki da cutar amma kuma gwamnatin taki biyan su hakkokin su.

Shugaban likitocin Aliyu Sokomba yace muddin gwamnati ta gaza wajen wareware matsalar nan da makwanni biyu masu zuwa, suma likitocin dake aiki a cibiyoyin kula da masu dauke da cutar COVID-19 za su bi sahun takwarorin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI