Tattaunawa da Dakta Mohammed Askira shugaban kungiyar likitocin Najeriya kan yajin aiki

Sauti 03:46
Ma'aikatar lafiya a Najeriya
Ma'aikatar lafiya a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Likitoci a Najeriya yau sun tsunduma cikin yajin aiki saboda abinda suka kira kin gwamnati na biyan su hakkokin su da kuma samar musu da kayan aiki, a daidai lokacin da annobar coronavirus ke cigaba da yaduwa a kasar, dangane da wannan batu ne Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dr Mohammed Askira shugaban kungiyar Likitocin Najeriya.

Talla

Kungiyar likitocin tace 'ya'yan ta dake aiki da gwamnatin Najeriya sun yanke hukuncin fara yajin aikin domin nuna rashin amincewar su da matakin na gwamnati, sai dai sun ce yajin bai shafi takwarorin su dake aiki a cibiyar yaki da masu fama da cutar coronavirus ba.

Akalla ma’aikatan lafiya 800 suka kamu da cutar coronavirus a kokarin da suke na yaki da cutar amma kuma gwamnatin taki biyan su hakkokin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI