Najeriya

Za mu ci gaba da bincike kan tsohon sarkin Kano Sanusi- Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

Gwamnan Kano da ke Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce za su cigaba da gudanar da bincike akan tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu dangane da matakan da ya dauka lokacin da yake rike da Sarautar jihar.

Talla

Ganduje wanda ke amsa tambayoyin manema labarai ya ce hukumar da ke sauraron ba’asin jama’a da kuma yaki da cin hanci da rashawa za ta cigaba da aikin da ta fara wajen binciken tsohon Sarkin.

Gwamnan ya ce za su cigaba da aiwatar da sauye sauye kan masarautun kano sakamakon kawo karshen kararrakin da tsohon Sarkin da kuma kungiyar Dattawan Kano suka shigar wadanda suka yiwa shirin tarnaki.

Ganduje ya ce bukatar su na aiwatar da sauye sauyen shi ne ganin an samar da cigaba a yankunan Jihar wanda hakan ya sa ya kirkiro sabbin Masarautu domin biyan bukatar jama’a.

Gwamnan ya ce annobar COVID-19 ta shafi tattalin arzikin jihar wajen rage kudaden shigar da ta ke samu abinda ya tilastawa gwamnati zabtare kashi 30 na kasafin kudin ta na wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.