Najeriya

Bai dace gwamnatin Najeriya ta yi barci ba- Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III
Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III YouTube

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban Jama’atu Nasril Islam a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar na III ya ce, ya kamata matsalar tsaro musamman a arewacin kasar ta hana gwamnatin kasar barci.

Talla

Sanarawar da Sakatare Janar na Jama’atu Nasril Islam, Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya fitar ta bukaci Rundunar Sojin Najeriya da ta kara kaimi wajen kawo karshen matsalar tsaro a kasar.

Sanarwar ta ce, bai kamata gwamnatoci a matakin tarayya da jiha su samu barcin dare ba saboda ci gaba da kisan kiyashin da ake yi wa jama’a tare da kona gidajensu da dabbobinsu a jihohin Borno da Kastina da Sokoto da Zamfara da Niger da wasu jihohin da suka hada da Adamawa da Kaduna da Taraba.

A ‘yan kwanakin nan, hare-haren ‘yan bindiga da na Boko Haram sun tsananta a arewacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da raba  wasu da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.