Buhari ya gargadi manyan hafsoshin soji kan tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFI Hausa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaidawa manyan hafsoshin tsaron kasar cewar bai gamsu da rawar da suke takawa wajen tinkarar matsalolin tsaron da suka yiwa kasar dabaibayi ba.

Talla

Bayan ganawar da Buhari ya yi da su Jumma'an nan a fadar sa, mai bashi shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno yace shugaban ya sake bayyana damuwar sa kan halin da kasar ke ciki.

Buhari yace shawo kan matsalar tsaro na daya daga cikin alkawuran da ya yiwa al’ummar Najeriya, bayan farfado da tattalin arzikin kasar da yaki da cin hanci da rashawa, amma samun nasara akan guda biyu ba tare da samar da tsaro ba zai zama aikin banza.

Monguno yace Buhari ya shaidawa hafsoshin cewar ba zai amince da cigaba da samun tabarbarewar tsaro a kasar ba, domin kuwa babu wanda ya tilasta masa nada su a mukamin.

Mai bada shawarar yace shugaban kasar ya shaidawa hafsoshin cewar al’amura na hannun su wajen sauke nauyin dake kan su na shawo kan matsalar tsaron da hana yaduwar makamai da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Harkoki tsaro sun sake tabarbarewa a Najeriya sakamakon karuwar hare haren mayakan book haram a arewa maso gabas da kuma Yan bindiga a arewa maso yamma, abinda yayi sanadiyar salwantar rayukan dimbin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.