Najeriya ta yi asarar Dala miliyan 48 a satar man fetur
Wallafawa ranar:
Katafaren Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ya ce, kasar ta yi asarar kudin da ya kai Dala miliyan 48 ko kuma Naira biliyan 17 wajen satar mai a cikin wannan shekara.
Shugaban kamfanin man, Mele Kyari ya bayyana haka a wani taro da ya gudanar a Majalisar Dattawa kan tallafin man da gwamnati ke sanyawa da kuma bukatar tace man a cikin gida.
Kyari ya ce, wannan adadi na Dala miliyan 48 ya sha banban da asarar da Najeriya ta yi ta Dala miliyan 825 a shekarar 2018 da Dala biliyan 725 a shekarar da ta gabata.
Shugaban kamfanin ya ce, matakan da suke dauka wajen gadin bututun man ya taimaka wajen hana barayi fasawa suna satar man.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu