Najeriya

Gwamnan Edo ya koma PDP daga APC

Gwamnan Edo Godwin Obaseki
Gwamnan Edo Godwin Obaseki Daily Trust

Gwamnan Jihar Edo da ke Najeriya Godwin Obaseki ya sauya sheka daga Jam’iyyarsa ta APC zuwa PDP kwanaki bayan hana shi sake takarar da aka yi.

Talla

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar jami’ansa da magoya bayansu zuwa Cibiyar Jam’iyyar PDP da ke Benin inda aka karbe shi hanu bibiyu.

Kafin wannan ziyarar, Obaseki ya gana da shugabannin PDP a Jihar ranar Laraba domin gabatar musu da aniyarsa ta shiga Jam’iyyar da kuma bukatar ba shi kujerar takara a zaben da za ayi a wannan shekara.

Rikici tsakanin Obaseki da ubangidansa kuma shugaban Jam’iyyar APC ta kasa Adams Oshimhole ya yi kamari, abin da ya sa Jam’iyyar ta ki ba shi damar sake takara a cikinta, matakin da ya sanya shi ya fice daga jam'iyyar.

Tuni jiga-jigan Jam’iyyar PDP a Najeriya cikinsu har da shugaban Jam’iyyar ta kasa Uche Secondus da Gwamnan Rivers Nyesome Wike suka yi maraba da Obaseki wanda sauya shekararsa ta kara yawan Jihohin da PDP ke mulki.

A karkashin jagorancin Oshiomhole, Jam’iyyar APC ta rasa Jihohin Zamfara da Adamawa da Bauchi da Oyo da Benue.

Yanzu haka kotu ta amince da matakin dakatar da Oshiomhole daga jagorancin jam’iyyar sakamakon matakin da reshen Jam’iyyar a Jihar Edo ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI