Najeriya ta nuna bacin rai kan rushe ginin Diflomasiyyarta a Ghana
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Najeriya ta yi tir da matakin rushe gine-ginen Difilomasiyyarta 2 da ke birnin Accra na kasar Ghana tare da neman karin bayani daga gwamnatin kasar game da musabbin hakan.
Ministan harkokin wajen Najeriyar Geoffrey Onyeama da ke bayyana hakan a shafinsa na Twitter jim kadan bayan bayyanar batun rushe ginin Diflomasiyyar, ya ce wajibi ne Ghana ta dauki matakin kare lafiyar ‘yan Najeriya da ke cikin kasar.
A cewar Onyeama tuni gwamnatocin kasashen biyu suka fara tattaunawa kan batun wanda bayanai ke cewa anyi amfani da motar rusau wajen niqe gine-ginen Diflomasiyyar Najeriyar.
Kamfanin dillancin labaran Najeriyar NAN ya ruwaito cewa tuni al’ummar kasar ta Ghana suka fara farmakar ‘yan Najeriyar da ke cikin gine-ginen baya ga kwashe kayankinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu