Najeriya

Gwamnonin APC sun roki Buhari ya ceto jam'iyyar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency/Handout via REUTERS

Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya sun roki shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya yi wa Allah ya ceto jam’iyyar daga dimbin matsalolin da suka yi mata dabaibayi.

Talla

APC na fama da tarin matsaloli a matakin kasa da jihohi, lamarin da ya sa aka dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, yayin da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da kuma mataikmakin gwamnnan jihar Ondo, Agboola Ajayi suka sauya sheka zuwa PDP.

Kazalika akwai wasu fitattun ‘yan siyasa da su ma suka fice daga jam’iyyar a cewar rahotanni.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da wasu takwarorinsa guda biyu, sun gana da shugaba Buhari a ranar Litinin dangane da matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta.

Ganawar na zuwa ne sa’o’i 24 da shugaban Majalisar Dattawan kasar, Ahmed Lawan ya gana da shugaba Buhari duk dai a kan lamarin rikicin cikin gidan jam’iyyar ta APC.

A bangare guda, wasu mambobin jam’iyyar sun gudanar da zanga-zanga a Sakatariyar Jam’iyyar ta Kasa, inda suke kira da a kori daukacin mambobin Kwamiitn Zartaswar Jam’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI