Gwamnan Yobe ya zama shugaban majalisar APC
Wallafawa ranar:
Majalisar Zartaswar Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nada gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko bayan rusa Majalisar Gudanarwa da aka yi yau yayin wani taro da ke gudana yanzu haka a fadar shugaban kasa.
Mai taimaka shugaban kasa kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad ya sanar da daukar matakin a taron Jam’iyyar da aka kira domin dinke barakar da ta kunno kai a cikinta wadda take kokarin raba kan shugabanninta.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar da gwamnonin jihohi da ake zargin suna goyan bayan jigon Jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu basu halarci taron ba.
Wadanda aka tabbatar sun halarci taron sun hada da gwamnonin Jihohin Nasarawa da Niger da Jigawa da Filato da Imo da Kogi da Yobe da kuma Osun.
Sauran sun hada da na Jihohin Ogun da Lagos da Kwara da Kebbi da Kano da Kaduna da kuma Ekiti.
Jam’iyyar APC ta fada rikicin shugabanci tun bayan da kotun daukaka kara ta tababtar da dakatarwar da aka yi wa shugabanta Adams Oshiomhole, inda mutane da dama suka fito suna ikirarin cewa, sune halartattun shugabannin Jam’iyyar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyan bayansa ga jagorancin Victor Giadom a matsayin shugaban riko, matakin da ake ganin ya saba wa matsayin Bola Ahmed Tinubu da magoya bayansa wadanda ke goyawa Hilliard Eta baya, bayan an amince ya rike wa Sanata Abiola Ajimobi kujerar sakamakon rahsin lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu