Najeriya

Tsohon gwamnan Oyo ya rasu a Lagos

Abiola Ajimobi
Abiola Ajimobi premiumtimesng

Tsohon gwamnan jihar Oyo ta Najeriya, Sanata Abiola Ajimobi ya rasu yana da shekaru 70 bayan fama da jinya a wani asibiti mai zaman kansa da ke jihar Lagos.

Talla

Rahotanni sun ce, Ajimobi ya shafe tsawon makwanni kwance a dakin kula da marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali a asibitin.

Mutuwarsa na zuwa ne bayan mako guda da aka yada jita-jitar rasuwarsa, amma daga bisani aka bayyana cewa, yana nan da ransa.

A farkon watan Yuni ne aka kwantar da shi a asibitin bayan kamuwa da cutar nan wadda ta harbi miliyoyin mutane tare da lakume rayukan kusan dubu 500 a sassan duniya.

Tsohon gwaman ya taba rike mukamin Sanata daga shekarar 2003 zuwa 2007, yayin da ya dare kan kujerar gwamnan Oyo a shekarar 2011, sannan aka sake zaben sa a shekarar 2015, abin da ya sa ya zama mutun na farko da ya yi wa’adin gwamna har sau biyu a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI