Bangaren Tinubu ya yi watsi da shugabancin APC

Bisa dukkan alamu tsugune bai kare a Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ba, ganin yadda magoya bayan bangaren Bola Ahmed Tinubu suka bayyana rashin amincewar su da rusa kwamitin zartarwa da kuma nada shugabannin riko a karkashin Gwamna Mai Mala na Jihar Yobe.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari a ofishin yakin neman zaben APC
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari a ofishin yakin neman zaben APC ayo Omoboriowo/Nigeria Presidency/Handout via Reuters
Talla

Wata sanarwar da bangaren ya rabawa manema labarai yace taron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta jiya haramcacce ne, saboda ba abi doka da oda ba, kuma suna shirin zuwa kotu domin kalubalantar matakin.

Sai dai Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu yayi watsi da barazanar zuwa kotun inda yake cewa labarin kanzon kurege ne.

Dangane da wannan dambarwa, tsohon Gwamnan Jihar Sokoto kuma daya daga cikin wadanda suka kafa Jam’iyyar ta APC Alh. Attahiru Bafarawa, yace dama ba’a kafa Jam’iyyar akan tafarki mai kyau ba, ganin irin kura kuran da aka tafka tun farko.

Bafarawa yace an kafa APC ne domin kawar da Goodluck Jonathan da kuma baiwa shugaba Muhammadu Buhari damar zama shugaban kasa ba tare da tsara yadda Jam’iyyar za ta yi jagoranci wajen magance matsalolin da suka addabi Najeriya ba.

Kuna iya latsa alamar sauti dake kasa don sauraron Bafarawa.

Tattaunawa da Attahiru Bafarawa danagene da rikicin APC

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI