Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya 9 a Borno

Rahotanni daga Najeriya sun ce mayakan Boko Haram sun kashe sojojin kasar guda 9 tare da Yan sa kai guda 2 lokacin da suka kai hari kan tawagar motocin da suke yiwa rakiya a Jihar Barno.

Sojojin Najeiya rike da tutar kungiyar Boko Haram
Sojojin Najeiya rike da tutar kungiyar Boko Haram REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP yace wasu fararen hula da dama sun bata sakamakon harin kwantar baunar da mayakn suka kai musu.

Rahotanni sun ce mayakan sun bude wuta kan tawagar motoci sama da 100 da sojojin ke yiwa rakiyar ne a wajen kauyen Komla dake kusa da Damboa wanda ke da nisan kilomita 55 daga Maiduguri.

Wani jami’in soji ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar harin na kwantan bauna ne, kuma mayakan sun yi amfani da manyan bindigogi da makaman roka.

Bayanai sun ce mayakan sun kwashi abinci da kayayyaki a motocin da suka kaiwa hari kafin su janye zuwa cikin dajin Sambissa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI