Buhari ya amice bude makarantun Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin bude makarantun kasar domin baiwa dalibai dake shirin kamala karatu damar yin jarabawan dake gaban su.

Wasu daliban makarantu a kasar cote d'ivore
Wasu daliban makarantu a kasar cote d'ivore REUTERS/Luc Gnago
Talla

Sanarwar da gwamnatin kasar ta gabatar yace daliban da suke ajin karshe za’a baiwa damar komawa karatun, yayin da daga ranar 1 ga watan Yuli za’a bude tafiye tafiye daga Jiha zuwa Jiha a fadin kasar.

Sakataren Gwamnati Boss Mustapha yace dokar hana fitar dare na nan daga karfe 10 na dare zuwa karfe 4 na asubahi, yayin da yayi barazanar rufe wasu kananan hukumomi 18 daga cikin 774 da ake da su a kasar saboda yaddan aka samu kasha 60 na masu dauke da cutar a Najeriya a cikin su.

Alkaluman Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya sun ce mutane 24,567 suka kamu da cutar, yayin da 565 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI