Dan wasan Najeriya ya lashe gasar RFI-FRANCE 24

Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen,ya lashe kyautar Marc-Vivien Foé 2020 na RFI-FRANCE 24
Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen,ya lashe kyautar Marc-Vivien Foé 2020 na RFI-FRANCE 24 AFP

Dan wasan gaba na tawagar Super Eagle ta Najeriya Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka na Marc-vivien Foé na shekarar 2020.

Talla

Ita dai wannan gasar da ke dauke da sunan tsohon dan wasan Kamaru Marc – vivien Foé da ya gamu da ajalinsa a filin wasa a Faransa, hadin guiwar kafar Talabijin din France 24 da Radion France International RFI ke shiryata tun a shekarar 2011 kuma duk shekara domin karrama Foé.

Gasar da ke maida hankali kan bajinta da dan wasa ya nuna a gasar Ligue 1 na kasar Faransa, a wannan karon dan wasan Najeriya da ke buga tamola a Lille ya yi nasarar lashe gasar bayan duke abokan karawarsa Islam Silimani dan kasar Algeria dake wasa a Monaco da kuma dan kasar Moroco Yunis Abdelhamid dake wasa a stade de Reims.

Victor Osimhen ya kuma kafa tarihin mafi karancin shekaru da ya taba lashe gasar, wato shekru 21.

Duk da tsaiko da annobar koronavirus ta haifar a sabgar ta wasanni, Victor Osimhen ya zura kwallaye 13 sannan ya taimaka anci kwallo har sau 4 a wasanni 27 da ya buga a wannan kaka, abin da ya bashi damar lashe gasar da gagarumin rinjaye wato maki 284, inda abokan karawarsa suka samu maki 95 da kuma 89.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.