Ma'aikatan agaji sun roki gwamnati ta ceto su daga Boko Haram

Sojojin Nijar dake yaki da Boko haram a yankin Bosso
Sojojin Nijar dake yaki da Boko haram a yankin Bosso ISSOUF SANOGO / AFP

Wasu Ma’aikatan agaji guda 4 da ma’aikacin tsaro guda sun bukaci Gwamnatin Najeriya da ta yiwa Allah ta kubutar da su daga hannun kungiyar Boko Haram wadda tayi garkuwa da su yanzu haka.

Talla

Wani faifan bidiyo dake dauke da mutanen da Jaridar Daily Trust ta samu ya nuna yadda mutanen ke zaune a tabarma suna mika rokon su ga hukumomin Najeriya.

Jaridar tace ma’aikatan sun fito ne daga kungiyar ‘Action Against Hunge’r da ‘Rich International’ da ‘International Rescue Committee’ da hukumar agajin gagagwa ta jihar Borno.

Bidiyon ya gabatar da Abdulrahman Babagana wanda yace shi ma’aikacin hukumar agajin gaggawar Jihar Barno ne, da aka kama akan hanyar Monguno zuwa Maiduguri, sai kuma Abdulrahman Dungus da yace shi ma’aikacin kungiyar ‘Rich International’, sannan Joseph Prince Joseph Prince da yace shi ma’aikacin tsaro ne a kamfanin ‘Alje Security Organisation’.

Sauran sun hada da Ishaiku Yakubu na kungiyar ‘Action Against Hunger’ da Luka Filibus na kungiyar ‘International Rescue Committee’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI