Najeriya

An tsinci gawar yarinyar da aka yi wa fyade a Masallaci

Matsalar fyade ta ta'azzara a sassan Najeriya.
Matsalar fyade ta ta'azzara a sassan Najeriya. Daily Trust

An tsinci gawar wata karamar yarinya mai shekaru 6 a cikin wani Masallaci da ke jihar Kaduna ta Najeriya bayan wasu kattai sun yi mata fyade har lahira.

Talla

Lamarin ya auku ne a ranar Juma’ar da ta gabata a unguwar Kurmin Mashi da ke gefen babbar hanyar Nnamdi Azikwe a karamar Hukumar Arewacin Kaduna.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce kawo yanzu babu wanda aka cafke da ake zargi da hannu a aika-aikar, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da gudanar da bincike.

Masallatai a jihar Kaduna na ci gaba da kasancewa a rufe sakamakon dokar hana taruwar jama’a wadda aka kafa don hana bazuwar cutar coronavirus, yayin da aka gano gawar yarinyar da misalin karfe 3:20 na yamma a cikin Masallacin.

Matsalar fyade ta ta’azzara a ‘yan kwanakin nan a sassan Najeriya, abin da ya sa kungiyoyi daban daban ke kira ga mahukunta da su samar da dokar kashe duk wanda aka samu da aikata laifin fyaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI