Buhari ya jaddada gina bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada matsayin gwamnatin sa na aiwatar da gina bututun iskar gas wanda zai tashi daga Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano domin saukakawa jama’a samun sinadarin cikin lokaci kuma kamar yadda aka tsara.

An fara gina bututun iskar Gas da zai taso daga Ajaokuta zuwa Kuduna da Kano a Najeriya
An fara gina bututun iskar Gas da zai taso daga Ajaokuta zuwa Kuduna da Kano a Najeriya © Nigeria Presidency
Talla

Yayin da yake kaddamar da fara aikin ta kafar bidiyo a Ajaokuta dake Jihar Kogi da kuma Rigachikum dake Jihar Kaduna, Buhari yace aikin na da matukar muhimmanci ga Yan Najeriya saboda haka ya zama dole a samu nasarar sa.

Shugaban ya umurci kamfanin man NNPC da abokan su wajen gudanar da aikin da su jajirce wajen tabbatar da ganin an gudanar da aikin wanda ke cikin shirin ayyukan gwamnatin san a inganta rayuwar jama’a.

Buhari yace sun yi Yan Najeriya alkawarin fadada aikin samar da iskar gas saboda amfanin jama’a a gidaje, saboda haka babu dalilin gazawa a ciki.

Shugaban yace bayan wannan aikin, akwai kuma wanda ke gudana tsakanin Escravos zuwa Lagos da Obiafu zuwa Obrikom.

Buhari yayi amfani da bikin wajen kalubalantar yan kasuwa da su zuba jari wajen ganin an ci moriyar iskar gas din da Allah Ya wadata kasar da shi, yayin da ya yabawa gwamnatin China da bankuna da kuma kamfanonin da suka zuba jari wajen aikin.

Shugaban yace an bada kwangilar aikin ne akan Dala biliyan 2 da miliyan 592, kuma kashi na farko zai ci kilomita 303.

Shugaban kamfanin man Najeriya Mele Kyari yace aikin zai taimaka wajen daukar bututun zuwa sassan arewacin Najeriya daga Naija Delta zuwa Gabashi da Yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI