Najeriya-Coronavirus

Gwamnatin Najeriya za ta killace kananan hukumomi 18

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta garkame kananan hukumomi 18 a sassan kasar, wadanda bincike ya nuna cewar suna dauke da kashi 60 na mutanen da suka kamu da cutar coronavirus.

Taron jama'a a wani yankin birnin Legas, yayin hada-hadar kasuwanci.
Taron jama'a a wani yankin birnin Legas, yayin hada-hadar kasuwanci. Reuters / Akintunde Akinleye
Talla

Shugaban kwamitin yaki da annobar ta coronavirus a Najeriyar, kuma sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha ne ya sanar da shirin daukar matakin, jim kadan bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari kan halin da ake ciki kan kokarin dakile annobar.

Boss Mustapha ya ce gwamnatoci a matakan jiha da kuma kananan hukumomin da lamarin ya shafa ne za su aiwatar da matakin killace yankunan da aka fi samun masu kamuwa da cutar ta coronavirus.

Mafi rinjayen kananan hukumomin da za a killace dai a jihar Legas suke, yayinda ragowar ke sauran jihohi.

Wasu daga cikin kananan hukumomin 18 sun hada da Eti-Osa, Ikeja, Apapa, Surulere da Mushin dukkaninsu a Legas, yayinda sauran suka hada da Nasarawa a Kano, karamar hukumar Katsina a jihar Katsina, karamar Hukumar Bauchi dake jihar at Bauchi, sai kuma Dutse dake jihar Jigawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI