Najeriya-Coronavirus

Rahoto kan matakin gwamnatin Najeriya na sassauta dokar takaita walwala

Wata matashiya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a kasuwar Dutse Alhaji dake Abuja a Najeriya. 2/5/2020.
Wata matashiya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a kasuwar Dutse Alhaji dake Abuja a Najeriya. 2/5/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Najeriya ta sanar da yin sassauci a game da dokar takaita walwala da aka kafa domin yaki da annobar COVID-19 a kasar.

Talla

A karkashin wannan sassauci, za a bude wani bangare na makarantun bokon kasar, tare da bai wa jama’a damar yin zirga-zirga a tsakanin jihohi a wasu kebantattun lokuta.

Sai dai kamar yadda za a ji a rahoton wakilinmu Muhammad Kabiru Yusuf, akwai yiwuwar gwamnati ta killace wasu kananan hukumomi dake Legas, Abuja, Kano da wasu karin jihohi lura da yadda wannan cuta ke ci gaba da ta’azzara a cikinsu.

Rahoto kan matakin gwamnatin Najeriya na sassauta dokar takaita walwala

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI