Shirin Kasuwa akai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba, ya maida hankali ne kan kanana da matsakaitun masana’antu, wanda alkaluman hukumar kasuwanci ta duniya ke nuna su ke da kashi 90 na harkokin kasunci da ke gudana a fadin duniya, kuma suke samar da kashi 70 na ayyukan yi, kana suke samar da kashi 50 na tattalin arzikin a ma’aunin GDP, da kuma yadda matasa ke dogaro da kai a Najeriya.
Sauran kashi-kashi
-
Kasuwanci Najeriya - An kaddamar da Matatar man Dangote mafi girma a duniya Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne kan kaddamar da katafariyar matatar Man Attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote a anguwar Lekki dake birnin Legas a kuduncin Najeriya.24/05/2023 10:22
-
Kasuwanci Tasirin aikin hakar mai a Nasarawa ga arewacin Najeriya Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan kaddamar da aikin hakar man fetur da aka gano a karamar hukumar Obi ta Jihar Nasarawa dake tsakiyar Najeriya.03/05/2023 09:53
-
Kasuwanci Najeriya ta sake tsundama cikin hauhawan farashin kayayyaki Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mai da hankali ne kan rahotan Hukumar Kididdiga ta Najeriya NBS da ta ta shelanta sake tsundumar kasar cikin wani kangin hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni, lamarin da ya jefa al’ummar kasar musamman masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.26/04/2023 10:01
-
Kasuwanci Matsin tattalin arziki ya haifar da tashin farashin kayayyaki a Ghana Shirin 'Kasuwa kai miki dole' na wannan makon ya leka kasar Ghana wadda a yanzu haka ke fama da matsin tattalin arziki irin wanda ta jima ba ta ga irinsa ba.19/04/2023 09:50
-
Kasuwanci Kasuwar Mile 12 dake Legas ta kayyade farashi saboda watan Ramadana Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida da hankali ne kan yadda farashin kayan masarufi ke hauhawa a lokacin azumin watan Ramadana a kowace shekara musamman a manyan biranen Najeriya. A mafiya yawan lokuta farashin kayayyakin masarufi, kayan abinci da na sha, na fuskantar tashin gwauron zabo bisa la’akari da bukatun kayan don yin amfani da su a lokacin azumi.14/04/2023 10:33