Rikici ya barke kan daukar ma'aikata dubu 774 a Najeriya

Wata Takaddama mai zafi ta barke tsakanin Yan Majalisun Najeriya da ministan kasa a ma’aikatar kwadago kan shirin gwamnati na daukar ma’aikata dubu 774 daga kowacce karamar hukuma dake kasar.

Lokacin wata hatsaniya a Majalisar tarayyar Najeria
Lokacin wata hatsaniya a Majalisar tarayyar Najeria Reuters
Talla

Sanarwar da ministan Festus Keyamo ya rabawa manema labarai, tace Yan Majalisun sun nemi karbe gurabun ayyukan, bayan an riga an basu gurabu 116,100 wanda shine kashi 15 amma Ministan yaki amincewa da bukatar su, abinda ya haifar da mahawara mai zafi a zauren Majalisar.

Ministan yace ba zai bada kai bori ya hau ba wajen karawa Yan Majalisun gurabun ayyukan wadanda aka shirya domin talakawan dake fadin kasar, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari kadai ke iya dakatar da shirin, bayan Yan Majalisun sun sha alwashin hana gudanar da shi.

Keyamo wanda ya sha alwashin sai inda karfin sa ya kare wajen ganin an tababtar da gaskiya wajen daukar ma’aikatar, ya amince da shigar da wakilan kungiyar Kiristoci da ta Musulmai da matasa da Sarkunan Gargajiya da kungiyoyin fararen hula da kuma direbobin motoci wajen ganin anyi gaskiya wajen dibar ma’aikatan a kowacce karamar hukuma.

Yan Najeriya sun dade suna korafi kan yadda samun aiki a kasar ke da matukar wahala ganin yadda manyan jami’an gwamnati da Yan Majalisu ke mamaye gurabun ayyukan wajen baiwa na kusa da su.

Minister Keyamo ya sha alwashin cewar a wannan karo ba zai bada kai bori ya hau ba, domin ya sha rantsuwar tabbatar da ganin Yan Najeriya da suka cacanta daga kowanne bangare sun samu gurabun aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI