Najeriya

A karon farko 'yan Najeriya sama da 750 sun kamu da coronavirus a rana 1

Wasu 'yan Najeriya a Abuja yayin jiran yi musu gwajin cutar coronavirus.
Wasu 'yan Najeriya a Abuja yayin jiran yi musu gwajin cutar coronavirus. AFP

A Karon farko Najeriya ta samu mutane mafi yawa da suka kamu da cutar coronavirus a rana guda, inda a jiya aka samu mutane 790, abinda ya kawo adadin Yan kasar da suka harbu da cutar zuwa 26,484, kana kuma 603 sun mutu.

Talla

Hukumar yaki da cututtukan kasar tace daga cikin sabbin mutanen 790, 166 sun fito ne daga Jihar Delta, sai 120 a Lagos, 66 a Enugu, 65 a Abuja, 60 a Edo, 43 a Ogun da kuma 41 a Kano.

Sauran sun hada da 39 a Kaduna, 33 a Ondo, 32 a Rivers, 29 a Bayelsa, 21 a Katsina, 20 a Imo, 18 a Kwara, 11 a Oyo, 10 a Abia, 6 a Benue, 4 a Gombe, 2-2 a Yobe da Bauchi da Kebbi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.