Najeriya

Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau saboda rikici

Gwamnan Jihar Bauchin Najeriya, Bala Mohammed ya dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman saboda rikicin filin noma da kiwo da ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara a kauyen Malunga da ke Zadawa Misau.

Gwamnan JIhar Bauchi Sanata Bala Muhammad.
Gwamnan JIhar Bauchi Sanata Bala Muhammad. RFI Hausa / Shehu Saulawa
Talla

Gwamnan ya ce, Sarkin tare da Hakimin Chiroma da Dakacin Zadawa da wasu saranakun gargajiya za su ci gaba da fuskantar dakatarwa har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan musabbabin rikicin na filayen kiwo da noma.

A ranar Litinin da ta gabata ne tarzoma ta barke a kauyen Malunja da ke Zadawa a Karamar Hukumar Misau biyo bayan sabanin da aka samu tsakanin makiyaya da manoma, yayin da ake zargin cewa, jami’an gwamnatin karamar hukumar na da hannu a cikin lamarin saboda muradinsu na mamaye filin da ake takaddama a kai.

Wannan matakin ne ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya har aka samu asarar rayuka tara.

Gwamna Bala ya ce, bayanan da suka samu sun nuna cewa, sakacin sarakunan gargajiyar ne ya yi sanadin barkewar rikicin.

Yanzu haka kwamitin binciken da aka kafa don gudanar da bincike kan lamarin zai gabatar da sakamakonsa nan da makwanni uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI