Mun baiwa Najeriya tallafin dala miliyan 41 don yakar coronavirus - Amurka
Gwamnatin Amurka ta sanar da baiwa Najeriya jumillar tallafin kudin da ya kai dala miliyan 41 da kusan rabi, kwatankwacin Naira biliyan 16, domin yakar annobar coronavirus.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da ta fitar a karshen mako, Amurkan ta ce tallafin kudin na baya Bayan nan, cigaba ne kan na sama da dala biliyan 8 da miliyan 100 da ta baiwa Najeriya cikin sama da shekaru 20, ciki har da tallafin sama da dala biliyan 5 da miliyan 200 ga fannin lafiyar kasar.
Yanzu haka dai jumillar mutane dubu 27 da 564, suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, dubu 11 da 69 sun warke daga cutar, yayinda 628 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu