Najeriya

Kusan mutane 400 sun warke daga cutar coronavirus a Najeriya cikin sa'o'i 24

Najeriya ta samu karin mutane 603 da suka kamu da cutar coronavirus, abinda ya sanya jumillar wadanda suka kamu da cutar a kasar kaiwa dubu 28 da 167, daga cikinsu kuma mutane 634 suka mutu.

Wani jami'in lafiya a Najeriya, yayin gwajin cutar coronavirus a birnin Abuja.
Wani jami'in lafiya a Najeriya, yayin gwajin cutar coronavirus a birnin Abuja. Kola Sulaimon/AFP via Getty Images
Talla

Rahoton da hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta wallafa a daren jiya asabar, yace an samu karin mutanen 603 ne a jihohi 18, kuma Legas ke kan gaba da adadin 135, sai Edo mai mutane 87, Abuja 73, yayinda aka samu sabbin kamuwa 67 a Rivers.

A bangaren samun waraka kuwa, karin mutane 393 gwaji ya tabbatar sun warke daga cutar ta coronavirus a jiya asabar, abinda ya sa jumillar adadin kaiwa dubu 11, da 462.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI