Najeriya

Sama da 'yan Najeriya miliyan 3 sun nemi guraben aikin N-Power dubu 400

Gwamnatin Najeriya tace sama da mutane miliyan 3 ne suka nemi gurbin ma'aikatan wucin gadi dubu 400 da za a dauka a karkashin shirin N-Power kashi na 3.

Wasu matasa dake neman aiki a Najeriya.
Wasu matasa dake neman aiki a Najeriya. Daily Trust
Talla

Mataimakiyar daraktar hulda da kafafen yada labaran ma'aikatar ayyukan jinkai da kuma kula da walwalar al'umma Rhoda Iliya ce ta bayyana halin da ake a karshen makon nan.

Mako guda kenan da gwamnati ta baiwa matasa damar neman gurbin aikin na N-Power.

Rahotanni sun ce tun da fari sama da ‘yan Najeriya miliyan 1 ne suka nemi gurbin na N-Power kasa da sa’o’I 48 da bude shafin neman aikin a Internet, tsakanin 26 zuwa 28 ga watan Yunin da ya gabata.

Kawo yanzu dai jumillar matasa ‘yan Najeriya akalla dubu 500 ne suka samu guraben aikin wucin gadin a karkashin shirin na N-Power kama daga kashin farko da ya kunshi mutane dubu 200 a watan Satumban 2016, da kuma kashi na 2 da ya kunshi mutane dubu 300, da aka soma dauka a watan Agustan 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI