Boko Haram-Najeriya

Boko Haram ta harbo jirgin agajin Majalisar Dinkin Duniya a Maiduguri

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da bayanan da ke cewa mayakan Boko Haram sun harbi jirgin sama mai saukar ungulu na jami’an agajinta, a garin Damasak da ke cikin jihar Borno a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula biyu da kuma raunata wasu da dama.

Wasu mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko haram a Najeriya.
Wasu mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko haram a Najeriya. Defencepost
Talla

Edward Kallon, shugaban ofishin ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, ya ce mutanen da suka rasa rayukansu ba daga cikin jami'an da jirgin ke dauke da su ba ne.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da farmakin na Boko Haram yayinda ya sha alwashin ci gaba da farmakar mayakan 'yan ta'addan wanda ya ce a yanzu haka suna ci gaba da fuskantar matsin lamba daga Sojin kasar da suke farmakarsu ba kakkautawa.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin bai fado ba, inda matukinsa ya yi gaggawar komawa cikin garin Maiduguri mai tazarar kilomita 150 daga inda farmakin ya faro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI