Najeriya

Gayyatar Magu aka yi ba kama shi ba - EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da almundahanar kudade ta Najeriya, EFCC, ta musanta rahotannin cewa jami’an tsaro sun kama mukaddashin shugabanta Ibrahim Magu.

EFCC ta musanta rahotannin kama shugabanta Ibrahim Magu.
EFCC ta musanta rahotannin kama shugabanta Ibrahim Magu. RFI / Pierre Moussart
Talla

EFCC ta fitar da sanarwar ce jim kadan bayan da itama hukumar DSS ta musanta rahotannin cewa, jami’anta ne suka kama Magu.

Cikin sanarwar da EFCC ta fitar, kakakin hukumar Dele Oyewale yace ba kama Magu aka yi ba, illa kawai shugaban ya bayyana ne bisa gayyata a gaban wani kwamitin bincike a fadar gwamnatin Najeriya dake Abuja, domin amsa tambayoyi kan yadda yake tafiyar da ayyukan hukumar.

Tuni dai itama hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya, ta musanta kama mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC, inda tace babu gaskiya a rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka wallafa cewar jami’anta sun kama Magu bisa wasu dalilai da ake alakantawa da laifukan almundahanar kudade.

Da yammacin ranar litinin din nan ce, wasu majiyoyi suka ruwaito cewar jami’an tsaron DSS sun yi awon gaba da Ibrahim Magu, labarin da akasarin kafafen yada labarai a ciki da wajen Najeriya suka dauka.

A waccan lokacin kuma rahoton kamen ya zo ne kwanaki kalilan bayan da ministan shari’a Abubakar Malami, ya zargi shugaban na EFCC da wasu laifuka ciki har da karkatar da makudan kudaden satar da aka kwato, tare da neman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kore shi daga mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI