Sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 75 a Maiduguri
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan Boko Haram 75 a cikin wata yunin da ya gabata a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da ta fitar a jiya, ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana cewa dakarun kasar sun yi aragama har sau 17 da mayakan na Boko Haram a cikin watan na yuni, inda suka kwace wasu motoci da makamai da dama daga mayakan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa dakarun sun kuma yi nasarar ceto fararen hula 35 da mayakan kungiyar suka yi garkuwa da su yayinda suka kame mayakan 4 ciki har da matan kwamnadan kungiyar ta boko haram shiyyar Adamawa da aka bayyana sunansu da Aishatu Manye da Kelune Mate.
Haka zalika sanarwar ta bayyana yadda Sojin na Najeriya suka kame dan leken asirin kungiyar ta Boko Haram mai suna Kawalu.
A baya-bayan nan ana ci gaba da yin kare jini biri jini tsakanin Sojin na Najeriya da mayakan Boko Haram bayan da Babban Hafson Sojin kasar Janar Tukur Burutai ya sha alwashin kammala kakkabe mayakan kungiyar ta'addancin cikin sauri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu