Najeriya ta janye matakin baiwa Makarantu damar budewa
Gwamnatin Najeriya ta sauya matsayin ta na sake bude makarantu domin bai wa daliban da ke shirin kammala karatu daukar jarabawa saboda abinda ta kira barazanar cutar coronavirus.
Wallafawa ranar:
Ministan ilimi Adamu Adamu ya ce sakamakon wannan mataki da gwamnati ta dauka, babu wani dalibin Najeriya da zai rubuta jarabawar kamala karatun sakandare da ake kira WAEC wanda Hukumar kula da jarabawar ta shirya gudanarwa daga ranar 5 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumba mai zuwa.
Ministan yace babu wani shiri na sake bude makarantun yanzu haka, saboda haka babu ranar gudanar da wannan jarabawa ta kamala karatun Sakandare bana.
Adamu yace Hukumar WAEC bata da hurumin sanya ranar da za’a bude makarantu a Najeriya domin kuwa ba hurumin ta bane, inda yace gwamnati ta gwammace daliban Najeriya sun kara shekara guda maimakon kamuwa da cutar coronavirus dake cigaba da dibar rayuka.
Ya zuwa wannan lokaci annobar coronavirus ta kama mutane 29,789 a Najeriya, ta kuma kasha 669.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu