Najeriya

Rundunar 'yan sanda za ta bincike Osinbajo kan kudin EFCC

Yemi Osinbajo tare da mai gidansa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Yemi Osinbajo tare da mai gidansa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Premium Times

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bukaci Sufeto Janar na 'yan sandan kasar da ya kaddamar da bincike kan zargin da ake yi masa na karbar kudade daga tsohon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC Ibrahim Magu.

Talla

Lauyan Osinbajo, Taiwo Osipitan ya bayyana zargin a matsayin yarfe da yunkurin bata wa mataimakin shugaban kasar suna, kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka rawaito.

Tuni wannan zargi ya mamaye Najeriya tun bayan tube Magu daga kujerarsa wanda kuma aka kaddamar da bincike kan ayyukansa.

Wata kafar yada labaran intanet da ake kira PointBlank News da Jackson Ude, tsohon daraktan ayyuka na musamman a karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ke wallafawa, ta ce Ibrahim Magu ya salwantar da Naira biliyan 39 daga cikin kudaden da hukumar ta kwato daga barayin gwamnati, kuma daga cikin kudaden ya bai wa Osinbajo Naira biliyan 4.

Rahotan ya ce, Magu ya bai wa mataimakin shugaban kasar wadannan makudan kudade ne a ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi London domin duba lafiyarsa.

Tuni mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Laolu Akande ya yi watsi da zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.