Buhari ya amince da dakatarwar da aka yiwa Magu na EFCC a hukumance
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin dakatar da shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da mai Magana da yawun ministan shari’ar kasar Abubakar Malami, wato Umar Gwandu ya rabawa manema labarai ta ce dakatarwar da aka yiwa Magun zai ba da damar gudanar da bincike ba tare da haifar da wata matsala ba ga hukumar da shugaban kasa ya kafa.
Gwandu ya ce Buhari ya kuma amince da bai wa Daraktan ayyuka Mohammed Umar damar jagorancin hukumar har lokacin da za a kamala binciken da kuma yanke hukunci akan su.
Gwamnatin Najeriya na zargin Magu da karkata akalar wasu kadarori da kuma kudaden da ya kwato daga barayin gwamnati, kana da zargin cewar yana bijirewa umurnin nag aba da shi kamar yadda ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana.
Jami’an tsaron DSS suka kama shugaban Hukumar EFCC ranar litinin domin amsa tambayoyi, amma kuma gwamnatin Najeriya tace gayyatar sa akayi, duk da yake har ya zuwa ranar juma’ar nan yana tsare ba tare da zuwa cikin iyalan sa ba.
Wata jaridar kasar ta zargi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da karbar naira biliyan 4 daga hannun Magu lokacin da yake rike da mukamin mukaddashin shugaban kasa, amma Osinbajo ya musanta zargin inda ya bukaci Sufeto Janar na Yan Sanda Adamu Muhammad da ya gudanar da bincike kan lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu