Buhari ya sa hannu kan kasafin kudin Najeriya da aka yiwa kwaskwarima
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan sabon kasafin kudin shekarar 2020 da aka yiwa gyarar fuska sakamakon annobar coronavirus wadda ta tilasta sake fasalin sa.
Wallafawa ranar:
Buhari ya sanya hannu akan kasafin na kusan naira tiriliyan 11 yau bayan Majalisar dokoki ta amince da shi, a wani biki da ya samu halartar shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal da shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da ministocin kudin kasar da na kasafin kudi da Gwamnan Babban Bankin Najeriya.
Shugaban ya ce nan da karshen wannan wata za’a bai wa ma’aikatun gwamnati da hukumomi kashi 15 na kasafin kudin su domin ganin an kama aiki gadan gadan.
Zabtare kasafin kudin dai zai shafi manyan ayyuka da dama da Majalisa ta amince da su a watan Maris da ya gabata, kafin barkewar wannan annoba ta COVID-19 wadda ta yiwa tattalin arzikin Najeriya da sauran kasashen duniya illa.
Najeriya dai ta dogara ne da sayar da man fetur wajen samun akasarin kudaden shigar ta, yayin da gwamnati ke kokarin karkata akalar kasar zuwa noma da karbar haraji domin samun Karin kudaden shiga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu