Turkiya

Erdogan ya mayar da wurin tarihi na Hagia Sophia babban Masallaci a Turkiya

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar za a bai wa al’ummar Musulmin kasar damar gudanar da ibada a daya daga cikin wuraren da Hukumar UNESCO ta bayyana a matsayin wurin tarihi da ake kira Hagia Sophia wanda zai koma zama Masallachi, matakin da ya haifar da suka daga shugabannin kiristocin duniya.

Katafaren wajen tarihi na Hagia Sophia.
Katafaren wajen tarihi na Hagia Sophia. Reuters
Talla

Daukar matakin shugaba Erdogan ya biyo bayan hukuncin kotun koli wadda ta soke matsayin ginin da aka yi a karni na 6 wanda aka mayar gidan tarihin da baki daga kasashen duniay ke ziyarta kafin daukar wannan sabon matakin mayar da shi Masallachi.

Shi dai wannan katafaren ginin da Masarautar kiristoci ta Byzantine ta gina a matsayin mujami’a, an mayar da shi Masallachi ne a karon farko a shekarar 1453 bayan da aka kafa Daular Ottoman da ta samu nasarar yaki a Costantinople.

A shekarar 1934 babbar kotun mulkin Turkiya ta soke matsayin Majalisar gudanarwar kasar wajen bayyana Hagia Sophia a matsayin Masallachi, abinda ya sa aka mayar da shi gidan tarihi da kuma baiwa mabiya addinai daban daban damar ziyara da kuma gudanar da ibada a ciki.

Sabon matsayin da kotun koli ta dauka da kuma rattaba hannun da shugaba Recep Tayyip Erdogan yayi ka iya haifar da matsala da kuma lalacewar dangantaka tsakanin Turkiya da wasu kasashen duniya.

Kafin dai daukar wannan mataki kasar Amurka ta hannun Mike Pompeo ta gargadi Turkiya wajen sauya gidan tarihin zuwa Masallachi, kamar yadda Hukumar UNESCO da shugabannin kiristoci da dama suka nuna rashin amincewar su.

Tuni aka fara samun martani daga sassa daban daban bayan hukuncin kotun, ciki harda kasar Girka wadda ta bayyana matakin a matsayin takalar fada a bayyane.

Ita kuwa mujami’ar Rasha cewa tayi Turkiya ta bijirewa bukatar miliyoyin kiristocin dake duniya wajen sauya matsayin ginin zuwa Masallachi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI